JIRNADU THEMAN IBRAHIM - Born to win_Gidan aure Songtexte

Verse 1
Idan mahaifin ka ya kwabe ka akan shaye shaye
Kada ka kai shi kad ka kai shi a gidan aure
Idan jatumar ki ta kwabe ki akan yawon banza
Kada ki kai shi kad ki kai shi a gidan aure

Chorus
Kada ka kai gida kada ki kai gida
Kada ka kai shi kada ki kai shi a gidan aure

Verse 2
Idan mahaifin ka ya kwabe ka akan dauke dauke
Kada ka kai shi kad ka kai shi a gidan aure
Idan jatumar ki ta kwabe ki akan guna guni
Kada ki kai shi kad ki kai shi a gidan aure

Verse 3
Idan mahaifin ka ya kwabe ka akan rashin shawara
Kada ka kai shi kad ka kai shi a gidan aure
Idan jatumar ki ta kwabe ki akan rashin hakuri
Kada ki kai shi kad ki kai shi a gidan aure

Verse 4
Menene maganar Allah ke koya mana kan zaman aure
Mu kaunace juna muyi hakuri cikin zaman aure
Menene maganar Allah ke koya mana kan zaman aure
Mu tallafe juna muyi shawara cikin gidan aure

Sai mu kai gida sai mu kai gida
Sai mu kai su sai mu kai su a gidan aure
Dieser text wurde 174 mal gelesen.